Hotuna Da Rahoton Taron ‘Dandalin Siyasa’ Kano 2014

Daga: Khalifa Ja’afar Gusau

image

Gwamnan Jihar Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso yake gudanar da bayani a wurin cin abinci (dinner)

image

Dandalin Siyasa Online Forum ke gudanar wa a watan september 2014 a gidan gwamnatin Jihar Kano.

image

A taron da muka saba gudanarwa karkashin wannan kungiya duk shekara mai suna ‘Dandalin Siyasa Online Forum’

image

Idan ba a manta ba mun yi taron 2013 a Zamfara, yanzu kuma gamu a Kano muna gudanar da taron wannan shekarar 2014.

image

A al’adar wannan kungiya duk jihar da muka sauka muna fara ziyara a ranar farko, wuraren da muke ziyara sune ‘gidan yari, gidan Marayu da gidan Sarkin gari.

image

A rana ta biyu kuma muna samun halartar kwararrin malamai domin kara muna ilmi da bamu shawarwari akan manufar mu ta kawo sauyi a siyasar Arewacin Nigeria, kamar wannan taron da mu kayi a Kano 2014 mun samu halartar Dr. Usman Muhammad, daga Jami’ar Abuja, ya gudanar da lecture akan ‘Democracy and the populist ideology’, sai Dr. Muhammad Hamisu Sani daga Jami’ar Bayero University Kano, ya gabatar da lecture akan ‘Media and Democracy’, daga karshe Professor Dalhatu Galadanci, Rector a Kano state polytechnic, yayi lecture akan ‘The Economy as a Northern challenge.

image

A rana ta uku kuma muna zagayawa a gari domin ganarwa idanun mu ayukan da gwamnatin jiha tayi domin mu fadawa duniya mu kuma yaba tare da jinjina mashi akan aikin,  hakika mun zagaya a garin Kano a ranar Lahadi tun misalin karfe tara na safe bamu dawo ba sai karfe biyar na marece, mun ga ayukan ban mamaki da dama amma wani abin mamaki ba mu ga kashi hansin cikin dari ba cikin ayukan da gwamna Kwankwaso yayi a wannan jiha cikin shekara uku.

image

Wurin da muka fara ziyara shine Kofar Nasarawa, anan muka tarar da wannan katafariyar gada wadda ake cema ‘flyover’ Jihar Kano ita ce farkon jihar da ta fara yin irin wannan gada a fadin Nigeria, an bada kwangilar ta akan kudi 5.9bn, kuma yanzu haka an kammala kashi tas’in chikin dari na aikin kamar yada kuke gani na ina tafiya a saman gadar.

image

A wurin ziyarar aikin gwamnatin Jihar Kano da Dandalin Siyasa Online Forum ta gudanar, mun tarar da wannan hanyar da akeyi a Gadon kaya, hanyar Mota ce mai tafiya a karkashin kasa, wato (Under pass road)

image

Bayan wannan unguwar mun kuma tarar da ana yin irinta a Kofar Kabuga, dukkan su gwamna Kwankwaso ya bada kwangular aikin su akan kudi 1.3bn ana sa ran kammala su zuwa karshen wannan shekarar December 22.

image

‘KWANKWASIYYA AMANA’ suna ne na taken siyasar Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, a zagayen da muka yi a karkashin ‘Dandalin Siyasa Online Forum’ na ganarwa idanun mu ayukan dA gwamnan yayi a jihar, hakaki mun ga ababe na ban mamaki wadanda ba muyi tsammanin akwai jihar da take iya yin haka a Najeriya ba, sai gashi mun gani a Jihar Kano, mun tabbatar da wannan suna na Kwankwasiyya Amana ba a baki yake ba, ba a saka Jar hula yake ba kuma ba suna ne da ake amfani da shi wurin yawon kamfen na siyasa ba. ‘KWANKWASIYYA AMANA’ suna ne na a gani a kasa, suna ne wanda ya amfanar da Al’ummar jihar Kano baki daya kuma suna ne wanda Gwamna Kwankwaso yayi amfani da shi ya barwa Al’ummar Kano tarihi mai amfani (Leagacy) wanda har duniya ta nade baza a manta da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ba.

image

Na san mai karatu zai tambayi cewa “wane irin tarihi ne ‘yan siyasar mu na wannan lokaci suke iya bari wanda za a rika iya tunawa dasu?”

image

Za ku ga hotunan gidaje gasu nan na hada wannan labari da su kamar yada hausawa ke cewa “gani ya kori ji”. To wadannan gidaje da kuke gani Gwamnan jihar Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya kirkiri sababbin unguwanni guda biyu a cikin jihar Kano.

image

Daya ya saka mata suna ‘KWANKWASIYYA CITY” Daya kuma ‘AMANA CITY’ Ita wannan Kwankwasiyya City tana da gidaje tun daga masu dakuna biyar har zuwa uku (5 to 3 bedrooms) Kimanin gidaje dubu daya da dari bakwai 1700 duk a cikin wannan area. Ita kuma ‘AMANA CITY’

image

Tana da gidaje daga masu daki uku zuwa masu daki biyu (3 to 2 bedrooms) suna da kimanin yawan dubu daya da dari biyu duk a cikin wannan unguwar. Idan aka hada yawan gidajen dake cikin Kwankwasiyya City da na Amana City zamu samu gidaje kimanin dubu biyu da dari tara a wadannan unguwanni guda biyu da Gwamna Kwankwaso yayi a jihar Kano cikin shekara uku.

image

Mun shiga mun zagaya ko ina idanuwan mu sun gani, kuma za a sayar da wadannan gidaje ga dukkak Al’ummar jihar Kano tun daga Maaikatan gwamnati, ‘yan kasuwa, ma’aikatan kamfanoni da sauran duk wani dan jiha mai bukata.

image

Wannan hanyar ita ake cema ‘Wuju wuju road’ hanya ce wadda duk shekara sai taci gidaje da rayukan Al’umma, shekaru da dama ana fama da wannan matsalar a wannan unguwa a jihar Kano, a ziyarar duba ayuka da “Dandalin Siyasa Online Forum” ta gudanar a jihar Kano muka tarar da Gwamnan wannan lokaci Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bada kwangilar gyaran ta akan kudi 8.7bln, yanzu haka ana akan aikin, wadannan magudanar ruwa (pipe) da kuke gani a hoto sune a kayi amfani dasu a matsayin magudanar ruwa, Mutun komi tsawon shi zai iya shiga cikin (pipe) din yayi tafiya ba tare da ya duka ba kamar yada kuke gani wani cikin (pipe) din a tsaye bai cimma karshen shi ba saida ya daga hannun shi.

image

kuma abin mamaki duk wadannan tarin ayuka da gwamna Kwankwaso yayi a wannab jihar bai taba ciyo bashi kona sisi daga wani wuri ba inji Kwamishinan ayuka wanda mu kayi wannan zagayen duba ayuka tare da shi.

image

Ilmi shine gishirin zaman duniya, hakika duk al’ummar da ta rasa ilmi ta halaka, a cikin ziyarar mu  ‘Dandalin Siyasa Online Forum’ mun tarar da abin mamaki a wannan bangare na ilmi, inda muka fara tarar da wannan gini na zaman dindindin (permanent site) na katafariyar Jami’a wadda gwamna Kwankwaso ya gina a Kano mai suna ‘NorthWest University’ Wannan jami’a ita ce ta farko da ta fara samun irin wannan gini a Nageriya, an bada kwangilar gina ta akan kudi 20bln yanzu haka kashi tas’in cikin dari 90% na aikin an kammala shi kamar yada kuke ganin yanayin ginin a hoto.

Ga kuma haifaffin ‘yan jiha fiye da dubu biyu 2000 gwamna Kwankwaso ya dauki nauyin kai su karatu a kasashen duniya, wasu za suyi degree wasu kuma degree na biyu (msc) a bangarora daban daban, a makarantu taban daban, a kuma kasashe daban daban.

image

Sai kuma institutions guda ashirin da biyu da ya gina a cikin Kano duk a cikin wadannan shekaru uku na shi. Kuma kar kayi tsammanin diyan masu kudi ne yake daukar nauyin karatun su, ko kusa! Mafi aksarin wadanda ke karatun diyan talakawa ne matukar dai ka hada sharuddan da ake bukata (qualification) to za ka shiga cikin masu cin wannan gajiyar. Wannan kawai ya isa ya nuna maka cewa gwamna Kwankwaso baya mulki irin mulkin ‘yan jari hujja (capitalism) mulkin in kana da abin hannu ka shigo ayi da kai, in kuma talaka kake to ka koma gefe ka zama dan kallo sai yada aka ga dama ayi da kai, Hakika mulkin Kwankwaso ba irin wannan mulki bane, Kwankwaso yana mulki ne mai amfanar da mai kudi da talaka (socialism).

Kuma abin ban sha’awa wadannan institutions ashirin da biyu da ya gina a Kano diyan talakawa ne ke karatu a ciki, domin jihar Kano tundaga primary har jami’a Gwamna Kwankwaso ya dauki nauyin karatun su kyauta (free education for all)

Ga jerin Sunayen Makaranta ashirin da biyu (22) da Gwamna Kwankwaso yayi a jihar Kano cikin shekara uku:-

 •  Kano Hospitality and Tourism Institute – Kano city.
 •  Kano Poultry Institute – Dambatta.
 •  Kano Institute of Qur’anic & Western Education – Kano city.
 •  Kano Fisheries Institute – Bagauda.
 •  Kano Farm Mechanization Institute – Dambatta.
 •  Kano College of Nursing and Midwifery – Madobi.
 •  Kano Corporate Security Training Institute – Gabasawa.
 •  Kano Reformatory Institute – Kiru.
 •  Kano Film Academy – Tiga Rock.
 •  Kano Informatics institute – Kura.
 •  Kano Sports Academy – Karfi.
 •  Kano Driving Institute – Kumbotso.
 •  Kano Irrigation Training Institute – Kadawa.
 •  Kano Entrepreneurship Development Institute – Dawakin Tofa.
 •  Kano Post Basic Midwifery School – Gezawa.
 •  Kano Institute of Horticulture – Bagauda.
 •  Kano Livestock Institute – Bagauda.
 •  Kano Development Journalism Institute – Kano city.
 •  School of Basic & Remedial Studies – T/Wada.
 •  Kano School of Health Technology – Bebeji.
 •  Governor’s College – Kano city
 •  Janbaki Girls Boarding College – Ungogo.

Ziyarar mu ta karshe mun shiga a wata tsohuwar makaranta mai suna ‘Sa’adatu Rimi College of Education’ kai kace sabowar ginawa ce saboda sabonta makarantar tare da gina wadan su sabbin blocks da gwamna Kwankwaso yayi a ciki.

Wadannan makarantu sune muka ga wadan su har muka shiga ciki muka ganarwa idanun mu, ba mu samu lokacin ganin su gaba daya ba saboda ba lokaci, amma Kwamishinan ayuka da mu kayi wannan zagayen da shi ya fada muna sunayen sauran da bamu samu halarta ba, wani abin sha’awa wadannan makarantu 17 suna zaune a permanent site saura biyar kuma ana kan gina masu permanent site din su. Yanzu haka an yaye dalibai diyan talakawa fiye da dubu bakwai a wadannan makarantu, kuma kar ku manta kyauta ake bada wannan karatun ga haifaffin jihar Kano fa.

Address by Zamfara Deputy Governor, Malam Ibrahim Wakkala Muhammad at Dandalin Siyasa Kano 2014

Daga: Khalifa Ja’afar Gusau

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s